Romans 3

Amincin Allah

1To, mece ce ribar zama Bayahude, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? 2Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.

3Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? 4Ko kaɗan! Bari Allah yǎ zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yǎ zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Gama a tabbatar kana da gaskiya, saʼad da ka yi magana,
ka kuma yi nasara saʼad da ka yi shariʼa.”
Zab 51.4

5Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) 6Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shariʼanta duniya? 7Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, don yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?” 8In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugunta don yǎ zama hanyar samun nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana zagi, cewa haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.

Babu Mai Adalci

9To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Alʼummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. 10Kamar yadda yake a rubuce cewa:

“Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;
11babu wani mai fahimta,
babu wani mai neman Allah.
12Duk sun kauce gaba ɗaya,
sun zama marasa amfani;
babu wani mai aikata nagarta,
babu ko ɗaya.”
Zab 14.1-3; Zab 53.1-3; M W 7.20

13“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,
harsunansu suna yin ƙarya.”
Zab 5.9

“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
Zab 140.3

14“Bakunansu sun cike da laʼana da ɗacin rai.”
Zab 10.7

15“Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
16hallaka da baƙin ciki suna koʼina a hanyoyinsu,
17ba su kuma san hanyar salama ba.”
Ish 59, 8

18“Ba sa tsoron Allah sam.”
Zab 36.1

19Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah. 20Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.

Adalci Ta Wurin Bangaskiya

21Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23gama duka su yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba—  26ya yi haka domin yǎ nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yǎ zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

27To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙaʼida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? Aʼa, sai dai ta wurin bangaskiya. 28Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. 29Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Alʼummai ba ne? I, shi Allahn Alʼummai ne ma, 30da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. 31To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.

Copyright information for HauSRK